– Wani babbar mai wasi a jihar Kaduna Sheik Auwal Albany ya mutu akan hannun masu kisan gila
– An rahot0 wanda hassashen da marigayi Sheik Albany ya yi kafin rasuwarsa ta tabbata
– Wani abun mai ba tausayi kwata kwata ne mutuwar wani babbar Malam a jihar Kaduna
Bashir Abdullahi El-Bash ya bayyana wanda, Malam yake cewa a lokacin yake duniya wanda, kai tsaye jam’iyyar Buhari za mu zaba, alkibilar mu kenan jama’a, amma fa ku sani Buhari ba shi da kudi, duk wanda zai yi aiki a madadin Buhari kada ya sa rai za a ba shi ko kwabo, kada kuma ya sa rai idan an fara mulki za a zo a yi masa fenti a gida.
Wani babbar mai wasi
Inda yake cewa kuma wanda: “Bari na fada muku, Buhari ko ya samu mulkin kasar nan ba zai iya gyara ta a cikin shekaru hudu ba, abinda muke bukata farko idan ya hau barna ta tsaya, saboda yanzu ba maganar gyara ake ba.”
KU KARANTA KUMA: Wani dan Najeriya ya maganta kan Buhari
Malam ya ci gaba da cewa, “irin yunwar nan da aka yi Buhariyya aka dinga cin su garin kwaki, to ko wanne talaka ya shirya sai an yi irin ta saboda gyara za’a yi, ya kamata mutane su gane don kar mutane su zo su ce, ku kuka ce mu zabi mutanen nan, amma ga shi an zo ana yunwa.
“Abinda nake so na fadawa talakawan mu shine, jama’a ko kun zabi Buhari, sai kun bi da addu’a, matakin farko. Wallahi kasar nan Allah ya azurta mu, amma an yi wawurar da idan Buhari ya hau hatta shi kan sa abinda yake tunani da za a shake wasu marasa gaskiya su amayo yana da wahala.
“Amma mu abinda muke fata a tsaida zalunci idan aka tabbatar an tsaida zalunci sai a koma shawarar ya za a yi a ci gaba? Saboda sun yi kaca – kaca da kasar, domin duk mutunin da zai yi shugabanci na kwana bakwai sai ya azurta kansa da zai yi shekaru dubu 70 ba zai yi talauci ba.”
Tabbas wannan hasashe na Malam ya zama gaskiya, sai dai mu ce Allah ya jikansa. Shi kuma Buhari Allah ya taimaka masa wajen cika burinsa na taimakon talakawa.
The post An bayyana akan Sheik Auwal Albany na garin Zariya kafin rasuwarshi (hoto) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
from Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM http://ift.tt/1Sg6GCD
via IFTTT
No comments:
Post a Comment