– Bashir Abdullahi El-Bash wani dan Najeriya da kuma wani marubuci akan shafin Facebook ya bayyana abinda yake faruwa da kasar Najeriya
– El-Bash yace wanda, an shigo da wata sabuwar yaudara don yi wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zagon kasa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari da wani tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo
Inda El-Bash ya fara kan sharhinshi, yace wanda, bincike ya nuna cewa iyalan ‘yan jari hajjar Najeriya wanda suka kware da iya yaudarar jama’a da satar dukiyar kasa sun shigo da wata sabuwar yaudara dan cimma burinsu na yi wa gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari zagon kasa.
KU KARANTA KUMA: Rashin jituwa ta auku a gwamnatin jihar Nasarawa
Suna amfani da ‘ya’yan su da matan su wajen hada kawance da iyalan Buhari, inda wasu har dauko jikokin Shugaba Buhari ko ‘ya’yansa suke domin kawo su gidajen su, wasu kuma sukan yawan kai wa matar Buhari ko ‘ya’yansa ziyara ko gayyatar su sabanin tsawon shekaru ba ma a saka iyalan na Buhari cikin wata sabga sai dai su yi isu-isu.
Bincike ya nuna cewa ‘yan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) wadanda suka dawo jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da wasu daga cikin jam’iyyar APC suna kashe makudan kudade domin kamun kafa wajen iyalan na Buhari kuma sukan tura matan su domin kamun kafa.
A don haka Buhari ka yi taka tsantsan dan wannan wani salo ne na yaudarar gwamnatin ka wani makirci na yan jari hujja ne yake tunkaro ka.
Sun yi tsawon shekaru suna zalunci a kasar nan hawanka mulki suna ganin cewa ka hana su sakat kuma sun samu matsala yanzu suna son su yi amfani da iyalanka domin kamun kafa, don kana ba su wani matsayi. Su ne na farko da za su fara yi maka zagon kasa dan mafi yawan su ba su dawo APC ba, sai da ka ci zabe.
Allah muna rokonka ka kare Buhari daga sharrin azzaluman Nijeriya ‘yan jari hujja. Amin.
The post Ku karanta abun mamaki wanda wani dan Najeriya ce game da gwamnatin Shugaba Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
from Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM http://ift.tt/26act6g
via IFTTT
No comments:
Post a Comment